Sayyid Nasrullah : Muna Rike Da Wasiyar Shugabannin Shahidan Hizbullah
(last modified Fri, 16 Feb 2018 18:09:15 GMT )
Feb 16, 2018 18:09 UTC
  • Sayyid Nasrullah : Muna Rike Da Wasiyar Shugabannin Shahidan Hizbullah

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya kara jaddada cewa Hizbullah tana kan wasiyan da shuwagabannin shahidan kungiyar suka bar masu.

Sayyid Nasurullah ya bayyana haka ne a wani jawabinsa da ya gabatar a dazu-dazun nan, don tunawa da shuwagabannin shahidan kungiyar a yakin da ta yi ta fafatawa da haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma yan ta'adda a cikin kasar Lebanon da kuma yankin. Sheikh Ragib Harb, Sayyid Abbas Musawi da kuma Imad Mugniyya na daga cikin shuwagabannin kungiyar wadanad suka yi shahada a hannun HKI.

A wani bangare na jawabinsa Sayyid Nasrullah ya yi kashedi wa kasashen yankin musamman kasashen Iraqi da Syria kan makirce-makircen shugaban kasar Amurka na yanzu Donald Trump wanda yake son mamaye arzikin mai da gas wannan Allah ya huwacewa yankin. 

Dangane da kasar Palasdinu kuma shugaban kungiyar ta Hizbullah ya bayyan cewa rashin amincewar Palasdinawa da matakin shugaban kasar Amurka na maida Qudus a matsayin cibiyar gwamnatin HKI wata babbar nasara ce, kuma yakamata a goyi bayansu har zuwa nasara.

A wani bangare na jawabinsa shugaban ya mika sakon taya murna ga Jumhuriyar Musulunci ta Iran kan cika shekaru 39 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.

Banda haka ya musanta zargin da wasu yan siyasar kasar Labanon suke yi na cewa kasar Iran tana shishigi a cikin harkokin kasar Labanon. Ya kuma bukaci masu fadar haka da su kawo misali ko da guda ne na irin shishigin da suke zargin Iran take yi a harkokin kasar Lebanon.