Pars Today
Manzon musamman na MDD a kasar Libya Ghassan Salamah ne ya bayyana damuwarsa akan yadda wasu sassa na kasar da su ka hada da birnin Tripoli su ka zama sansanonin 'yan ta'adda
Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin Fuqaha da ke tsakiyar kasar Libiya, inda suka kashe mutane tare da sace matasa da 'yan sanda.
Gwamnatin Libiya da ke da matsuguni a garin Tobruk a gabashin kasar ta sanar da mutuwar mutane uku ma'aikata a gidan samar da hasken wutan lantarkin kasar ta Libiya.
Majiyar labarai daga kasar masar sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta kuduri aniyar aikewa da sojojin kasar zuwa kasar Libya.
Gwamnatin hadin kan kasar Libya ta yi gargadi akan taron da aka yi a kasar Masar wanda yake nuna goyon baya ga Janar Halifa Haftar
Jami'an tsaron gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun kame gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin kudancin garin Sirt na kasar.
Mahukunta a Libiya sun sanar da cewar an sake gano wani babban rami mai dauke da gawawwakin mutane 110 a wani yanki da ke kusa da garin Sirt na kasar.
Gwamnan babban bankin kasar Libiya ya ce rikici da yakin cikin gida na janyowa kasar hasarar dala biliyan 48.6 a ko wata shekara
Ministan harakokin wajen kasar Aljeriya ya ce nan ba da jimawa ba kasashen Masar da Tunusiya gami da kasarsa za su gudanar da zama kan rikicin kasar Libiya a birnin Alkahira.
Wata majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da gano wani babban kabari mai dauke da tarin gawawwakin mutane a yankin yammacin garin Sirt na kasar.