Yakin Cikin Gida Ya Janyo Wa Libiya Hasarar Dala Biliyan 48
(last modified Fri, 12 Oct 2018 19:16:36 GMT )
Oct 12, 2018 19:16 UTC
  • Yakin Cikin Gida Ya Janyo Wa Libiya Hasarar Dala Biliyan 48

Gwamnan babban bankin kasar Libiya ya ce rikici da yakin cikin gida na janyowa kasar hasarar dala biliyan 48.6 a ko wata shekara

Kafar watsa labaran Alwasat ta kasar Libiya ta nakalto Sadiq al-Kabir gwamnan babban bankin kasar Libiya na cewa rikicin siyasa da kuma yakin cikin gida da kasar fuskanta na janyowa kasar hasarar dala biliyan 48.6 cikin ko wata shekara, a bangare guda kuma ga yadda farashin Danyan mai ya sabka a kasuwar Duniya, wadannan ababe sun yi tasiri na koma baya a tattalin arzikin kasar.

Yayin da yake bayyani kan kudaden da kasar ke samu ko wata shekara, gwamnan babban bankin kasar Libiya ya ce daga shekarar 2012 zuwa 2015 kasar na samun dala biliyan 53.2, amma a shekarar 2016, kudin sun ragu da kusan biliyan 4.6, sanadiyar rikicin siyasa da kuma yakin cikin gida da kasar ke fama da shi.

Al-Kabir ya ce duk da cewa a shekarar 2017, kasar ta kara yawan danyan man fetir din da take sayarwa a kasuwanin Duniya inda aka kwatamta da shekarun baya, to amma kudin shigar kasar ya ragu da kashi 71.3 % cikin dari inda aka kwatamta da abinda kasar ta samu a shekarar 2012.