Gwamnatin Masar Zata Tura Sojoji Zuwa Kasar Libya
Majiyar labarai daga kasar masar sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta kuduri aniyar aikewa da sojojin kasar zuwa kasar Libya.
Shafinn yanar gizo ta jaridar "Ra'ayul Yaum" ya nakalto wata majiyar sojojin kasar Masar tana cewa shugaban kasar Abdulfattah Assisi tare da Khalifa Haftar kwamandan sojojin da ake kira "rundunar kasar Libya" sun amince da hakan tare da shiga tsakani na gwamnatin kasar Hadaddiyar daular larabawa.
Labarin ya kara da cewa wasu sojojin Halifa Haftar tare da jami'an sojojin kasar Masar sun tattauna wannan batun a birnin Alkahira a ranar Laraba da ta gabata. Rahoton bai bayyana yawan sojojin da Masar zata aika zuwa kasar ta Libya ba, amma sojojin zasu fito ne daga rundunar da ake kira "Sa'iqa" ta kasar Masar.
Wasu rahotannin sun bayyana cewa Halifa Haftar yana da kudurin kwace birnin Tripoli babban birnin kasar daga hannun gwamnatin Hadin kan kasa wacce Fa'iz Suraj yake jagoranta. Gwamnatin Suraj dai ta nuna damuwarta da wannan labarin.