Pars Today
Kakakin sojojin kasar Libya masu biyayya ga Halifa Haftar ya sanar da cewa sun kama dan ta'addar kasar Masar mafi hatsari a garin Derna a jiya Litinin.
Shugaban gwamnatin hadin kan kasa a Libya Faiz Siraj, ya kori ministoci hudu daga cikin gwamnatinsa.
An sake rufe filin saman jiragen birnin Tripoli babban birnin kasar Libiya bayan sake barkewar rikici da kuma halba makamin iguwa a filin saukar jiragen saman.
Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Libiya, ya bayyana cewa akwai wuya a gudanar zabe kamar aka tsara a kasar ta Libiya.
Ministan harkokin wajen kasar Libiya ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin tallafa wa kasar Libiya a bangaren tsaro.
Manzon musaman na Majalisar Dinkin Duniya kan Kasar Libiya ya soki ayyukan gwamnatin hadin kai da Majalisar dokokin kasar Libiya
Majiyar tsaro daga kasar Libya ta ce an sami dawowar zaman lafiya a cikin birnin na Tripoli bayan an dauke wata guda ana fadace-fadace
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da cewa: Gumurzu da manyan makamai ya sake kunno kai a yankunan da suke gefen birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya sanar da cewa: 'Yan bindigan da basu mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba a kasar Libiya zasu fuskanci takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.