An Sake Rufe Filin Tashin Jiragen Saman Birnin Tripoli Na Libiya
An sake rufe filin saman jiragen birnin Tripoli babban birnin kasar Libiya bayan sake barkewar rikici da kuma halba makamin iguwa a filin saukar jiragen saman.
Rahotanin dake fitowa daga kasar Libiya sun ce a jiya Talata, ma'aikatar dake kula da filin sauka da tashi na jiragen saman birnin Tripoli ta sanar da rufe filin, bayan da fada ya sake barkewa tsakakin kungiyoyin matasan dake dauke da makamai da kuma halba makamin iguwa cikin daren litinin wayewar Talata a filin saukar jiragen saman na birnin tripoli fadar milkin kasar Libiya.
Bayan rufe filin jirgin na tsahon makoni biyu, a ranar Larabar da ta gabata ce aka sake buda filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Mitiga.
Kimamin wata guda da ya gabata ne rikici ya kuno kai tsakanin kungiyoyin matasa dake dauke da makami masu goyon bayan gwamnatin hadin kan kasar da kuma kungiyar nan mai dauke da makamai mai suna Liwa'i Sabi'i a birnin Tripoli na Libiya, kuma duk da cewa an cimma yarjejjeniyar sulhu tsakanin bangarorin biyu bisa shiga tsakanin MDD, a halin da ake ciki rikicin ya sake barkewa.
Ya zuwa yanku,wannan rikici ya salwanta rayukan mutum 117 da kuma jikkata wasu 383 na daban.