Sep 29, 2018 11:58 UTC
  • Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Tallafin Majalisar Dinkin Duniya A Bangaren Tsaro

Ministan harkokin wajen kasar Libiya ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin tallafa wa kasar Libiya a bangaren tsaro.

A jawabinsa a zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa karo na 73: Ministan harkokin wajen kasar Libiya Muhammad Siala ya bayyana cewa: Gwamnatin Libiya tana bukatar tallafin Majalisar Dinkin Duniya a fagen wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Muhammad Siala bai fito fili ya gabatar da bukatar kafa rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya da zata taimakawa jami'an tsaron Libiya a fagen wanzar da zaman lafiya da tsaro ba, amma ya jaddada cewa babbar bukatar kasarsa a halin yanzu ita ce ganin an wanzar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar ta Libiya 

Tags