MDD Ta Soki Ayyukan Gwamnatin Libiya
(last modified Fri, 28 Sep 2018 11:51:21 GMT )
Sep 28, 2018 11:51 UTC
  • MDD Ta Soki Ayyukan Gwamnatin Libiya

Manzon musaman na Majalisar Dinkin Duniya kan Kasar Libiya ya soki ayyukan gwamnatin hadin kai da Majalisar dokokin kasar Libiya

Ghassan Salamé manzon musaman na MDD kan kasar Libiya ya ce a halin da ake cikin kasar Libiya na bukatar shugaba da zai hada kan 'yan siyasar kasar, kuma Majalisar Dinkin Duniya ba za ta iya maye gurbin gwamnatin kasar ba.

Ghassan Salamé ya ce 'yan Majalisar dokokin kasar ba su damu da halin da kasar take ciki ba, kawai tunaninsu yadda za su ci gaba da zama a kan kujerunsu, saboda ayyukan da gwamnatin hadin kan ke yi bai dace da halin da kasar take cikin a yanku ba.

Salame ya ce tawagar da MDD ta tura kasar na iya kokarinta na ganin ta taimakawa kasar domin samar da gwamnatin demokaradiya da kuma za ta iya jagoranci na gari a kasar.