Pars Today
Majiyar sojojin kasar Mali ta bada sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar hallaka yan ta'adda 15 a wani sumamen da suka kai masu a garin Mupik a tsakiyar kasar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta bakin kakakinsa Stéphane Dujarric ya kira yi dukkanin bangarori rikici a kasar ta Mali da su mai da wukakensu cikin kube, su rungumi sulhu
Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta soma shirin gano wadanda ke kawo tarnaki a shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, domin kakaba masu takunkumi.
Kakakin Sojan Faransa a kasar Mali Patrik Steiger ne ya sanar da haka, ba tare da yin cikakken karin bayani akan yadda lamarin ya afku ba
Wata majiya a kasar Mali, ta bayyana cewa wasu kasashen yankin ne ke bayar da horo da kuma bayar da makamai ga masu kai hari a kasar
Dakarun hadaka dake kasar Mali sun sanar da hallaka 'yan ta'adda biyar a wani sumeme da suka kai sansaninsu a kusa da garin Tombouctou na arewacin kasar
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar sojan kasar ta Mali na cewa; An kashe fursunonin ne a lokacin da suke kokarin guduwa
Rundunar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Mali MINUSMA ta sanar da mutuwar sojojinta biyu da kuma jikkatar wasu 10 na daban a wani hari da aka kai sansaninsu na Aguelhok dake arewa maso gabashin kasar Mali.
Kotun kasa da kasa mai shari'ar laifuffukan yaki (ICC) ta sanar da kame daya daga cikin 'yan kasar Mali da ake zargi da aikata laifuffukan yaki da take hakkokin bil'adama da aka tafka a kasar Mali din.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani Otel dake cikin garin Bandiagara dake tsakiyar kasar Mali.