Pars Today
Fira ministan Mali ya bukaci hadin kan kasa a Mali tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.
Al'ummar yankin tsakiyar kasar Mali sun sanar da kafa wata kungiyar dakarun sa-kai masu dauke da makamai domin kare kansu daga hare-haren ta'addanci.
Mai magana da yawun Sojojin Faransa Patrik Steiger ya ce; An jikkata sojojin biyar ne a wani harin da aka kai musu yankin Kidal.
Kasar Kanada ta sanar da cewa za ta tura wasu jirage masu saukar ungulu su 6 bugu da kari kan wasu sojoji guda 250 don shiga cikin dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD da suke kasar Mali.
Tashar talabiji din France24 ta ambato majiyar tsaron Mali tana cewa wata nakiya da aka dasa a bakin hanya ta tashi da motar sojojin kasar a yankin Dioura.
Akalla Sojojin Mali 4 ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin nakiya a tsakiyar kasar
Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya kammala gajeren ran gadin da ya kaddamar a wasu kasashen nahiyar AFrika.
A rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yana nuni da cewa: Ana ci gaba da samun bullar matsalar tashe-tashen hankula a kasar Mali.
Majalisar Dinikin Duniya ta tabbatar da mutuwar wasu jami'an na kiyaye zaman lafiya hudu a Mali, a lokacin da motarsu ta taka wasu boma-bomai.
Ministan tsaron kasar Faransa ta sanar da hallakar sojojin kasar sa biyu sanadiyar tashin nakiya yayin motar su ke ficewa a kasar Mali.