Tashin Nakiya Ya Hallaka Sojojin Faransa Biyu A Mali
Ministan tsaron kasar Faransa ta sanar da hallakar sojojin kasar sa biyu sanadiyar tashin nakiya yayin motar su ke ficewa a kasar Mali.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Florence Parly ministan tsaron kasar Faransa a jiya Laraba cikin wani jababi da ta yi a zauren Majalisar dokokin kasar ta ce wata nakiya ta tashi da motar sojojin kasar a yayin da suke ficewa,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin mu biyu da kuma jikkatar wani na daban.
Tun a shekarar 2012 ne kasar ta Mali ta fada cikin rikici, bayan juyin milki sojoji, da kuma mamaye wasu yankunan arewa kasar da 'yan tawayen abzunawa tare da kungiyoyi masu da'awar jihadi suka yi.
A shekarar 2013, kasar Faransa da Majalisar dinkin duniya sun tura dakarunsu zuwa kasar ta Faransa domin taimakawa sojojin kasar fatattakar kungiyoyin 'yan tawayen da masu da'awar jihadi, bayan an kwace yankunan dake hanunsu, mayakan dake cikin kungiyoyi masu da'awar jihadi sun buya a cikin saharar kasar, inda har ya zuwa yanzu suke ci gaba da kai hare-haren sunkuru kan sojojin kasar ta Mali, da na Faransa gami da na MDD.