An Kai Hari Kan Wata Olel A Kasar Mali
Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani Otel dake cikin garin Bandiagara dake tsakiyar kasar Mali.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto wata majiya daga kasar Mali na cewa a jiya Laraba wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari kan wani Otel dake cikin garin Bandiagara tare da kashe mutum guda da kuma jikkata wasu biyu na daban.
Majiyar ta ce maharan su biyar ne kuma yayin da suka tunkari Otel din sun buda wuta kan wani jami'in tsaro dake gadin Otel din, lamarin da ya yi sanadiyar halakarsa.
Wannan Otel dake garin na Bandiagara, wuri ne na kai kawon ma'aikatan MDD da kuma na kungiyoyin kai agaji na kasa da kasa.
Tun daga skekarar 2015 ne yankunan tsakiyar kasar ta Mali ya fara fuskantar hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda.