Mali: An Kashe Fursunoni 14 A Wani Gidan Kurkuku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29712-mali_an_kashe_fursunoni_14_a_wani_gidan_kurkuku
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar sojan kasar ta Mali na cewa; An kashe fursunonin ne a lokacin da suke kokarin guduwa
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 07, 2018 13:42 UTC
  • Mali: An Kashe Fursunoni 14 A Wani Gidan Kurkuku

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar sojan kasar ta Mali na cewa; An kashe fursunonin ne a lokacin da suke kokarin guduwa

Sojojin kasar ta Mali sun ce; An Kame mutanen ne a tsakiyar garin, da nisan kilo mita 120 daga garin Mopti. Majiyar sojan ta ce za ta gudanar da bicike akan hakikanin abin da ya faru.

Yankin Mopti ya shahara da hare-haren kungiyoyi masu wuce gona da iri, musamman a cikin watannin bayan nan.

Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil'adama da su ka hada da kungiyar "Amnesty International' suna zargin gwamnatin Mali da yi wa fursunoni kisan gilla.

Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar da kuma bullar kungiyoyi masu dauke da makamai.