Pars Today
A jiya Lahadi ce sabon Fraiministan kasar Mali Samaila Bubeye Maiga ya gabatar da majalisar ministocinsa don tantancewa ga gaban majalisar dokokin kasar.
Shugaban kasar Mali ya jaddada aniyar sabuwar gwamnatinsa ta tabbatar da zaman lafiya da sulhu a yankin arewacin kasar da ke fama da tashe-tashen hankula.
Shugaba Ibrahim Bubakar Keita ya yi rantsuwa ne a yau Talata domin fara zango na biyu na shugabancin kasar ta Mali
Masu adawa da gwamnatin Bubakar Kaita na kasar Mali sun gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben da ya bawa shugaba Kaita damar ci gaba da mulkin kasar a karo na biyu.
Gwamnatin kasar Mali ta bayyana ranar da za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Mali.
Kotun da ke kula da kundin tsarin mulkin kasar Mali ta bayyana gamsuwarta da yadda aka gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu tare da amincewa da sakamakon zaben.
Yan adawa a kasar Mali sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a kasar.
Masana sun bayyana cewa shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Kaita yana da tarin matsalolin da yakamata ya warwaresu a zangon shugabancin kasarsa karo na biyu.
Magoya bayan dan takarar adawa Soumaila Cisse sun nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben shugaban kasar Mali zagaye na biyu da aka gudanar a jiya.
Dan takarar jami'iyyar adawa Soumaila Cisse ya ce al'ummar Kasar Mali ba za su lamince da murdiyar zabe ba, don haka al'umma "su tashi tsaye".