Fraiministan Kasar Mali Ya Gabatar Da Sabbin Majalisar Ministocinsa
A jiya Lahadi ce sabon Fraiministan kasar Mali Samaila Bubeye Maiga ya gabatar da majalisar ministocinsa don tantancewa ga gaban majalisar dokokin kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce Firaiministan ya nada ministoci 32 ne, 7 daga cikinsu sabbi ne sannan 11 daga cikinsu mata. Majalisar ministocin gwamnatin da ta gabata dai tana da ministocin 36 ne.
A cikin ministocin da aka canza akwai na harkokin waje wanda a wannan karon aka bawa Malama Mamissa Camara wacce kafin haka mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin diblomasiyya ne.
A ranar talatan da ta gabata ce shugaban kasa Bubakar Kaita ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa karo na biyu bayan ya lashe zabe zagaye na biyu da aka gabatar a cikin watan da ya gabata.