Shugaban Kasar Mali Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki
(last modified Tue, 04 Sep 2018 18:11:30 GMT )
Sep 04, 2018 18:11 UTC
  • Shugaban Kasar Mali Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki

Shugaba Ibrahim Bubakar Keita ya yi rantsuwa ne a yau Talata domin fara zango na biyu na shugabancin kasar ta Mali

Keita dan shekaru 73 ya lashe zaben shugabancin kasar ne zango na biyu da aka yi a ranar 20 Agusta. Bayan sauyi da aka samu a tsarin mulkin kasar, kowane zango na shugabanci ya koma shekaru biyar.

soumaila Cisse wanda ya kara da shugaba Keita a zaben, har yanzu bai yarda da ya sha kashi ba. A sanarwar da ya fitar a jiya Litinin ya sake nuna kin amincewa da sakamakon zaben na ranar 20 ga watan Agusta.

Daga lokacin da aka sanar da sakamakon zaben, kowane mako magoya bayan Cisse suna gudanar da Zanga-zangar kin amincewa.