Pars Today
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai harin wuce gona da iri kan rundunar sojin Masar a yankin Sina kusa da kan iyaka da yankin Zirin Gaza na Palasdinu, inda suka kashe soja guda.
Majiyar tsaro daga kasar ta Masar ta ce: A yau asabar ne aka kai harin akan wata motar soja mai sulke wanda ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu da kuma jikkata wani guda daya.
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya kai ziyarar aiki zuwa birnin Khartun na kasar Sudan a jiya Alhamis ya kuma gana da tokoransa na kasar ta Sudan Umar Hassan Al-Bashir.
Kungiyar ta gwagwarmayar musulunci ta bayyana amincewarta da shawarar da Masar ta bijiro da ita akan sulhu tsakanin bangarorin palasdinawa.
Majalisar Dokokin Masar ta amince da daftarin kudurin da aka gabatar mata na hana gurfanar da manyan jami'an sojin kasar a gaban kotu domin fuskantar shari'a.
Gwamnatin Masar ta rufe mashigar Rafah da ke tsakanin kan iyakar kasarta da yankin Zirin Gaza na Palasdinu lamarin da zai kara wurga al'ummar yankin Zirin Gaza cikin mawuyacin hali.
Majalisar dokokin kasar Masar ta amince da dokar sanya ido a kan shafuffukan sadarwa na zamani a kasar don bawa jami'an tsaron kasar damar hana lamaran kariya da kuma laifuffukan da ake aikatawa a irin wadannan shafuffuka.
Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin dauri kan wasu yan kungiyar Ikhwanul Muslimin na kasar saboda laifuffuka daban daban na nuna adawa ga gwamnain kasar.
Labaran da suke fitowa daga birnin Alkahira na kasar Masar sun bayyana cewa an ji fashewar abubuwa a kusa da tashar sauka da tashin jiragen sama na birnin kuma an ga harshen wuta na nagawa daga yankin.