Shugaban Kasar Masar Ya Gana Da Takwaransa Na Sudan A Kharthum
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya kai ziyarar aiki zuwa birnin Khartun na kasar Sudan a jiya Alhamis ya kuma gana da tokoransa na kasar ta Sudan Umar Hassan Al-Bashir.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayyana cewa shuwagabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu wadanda suka hada da matsalolilin gabas ta tsakiya da wadanda suka shafi kasashen biyu.
Wannan ziyara ita ce ta 6 wacce shugaban Assisi yake kaiwa kasar Sudan tun bayan zamansa shugaban kasar Masar a shekara ta 2014, kuma ita ce ta farko bayan ya fara wa'adin shugabancin kasar a karo na biyu a cikin watan yunin da ya gabata.
Sudan da Masar dai suna da sabani kan kogin Nili, rikicin yan tawaye na Darfur da kuma batun yankin Halaayib na bakin tekun malia ko red sea.
A ganawar shuwagabannin biyu a kasar Masar a cikin watan maris na shekarar da muke ciki sun fahinci juna a kan wasu lamura.