Hamas Ta Amince Da Shirin Suhlu Da Masar Bijiro Da Shi
Jul 19, 2018 12:38 UTC
Kungiyar ta gwagwarmayar musulunci ta bayyana amincewarta da shawarar da Masar ta bijiro da ita akan sulhu tsakanin bangarorin palasdinawa.
Wata tawagar Palasdinawa ta isa Masar domin sake samun bayani akan shawarar da gwamnatin Masar din ta bijiro da ita na sulhu tsakanin kungiyar Hamas da kuma gwamnatin kwarya-kwarya ta palasinawa.
Musa Abu Marzuq wanda jami'i ne na kungiyar ta Hamas ya shadawa kamfanin dillancin labarun Palasdinawa na Safa cewa; Shirin na Masar za a aikwatar da shi ne daga mataki zuwa wani mataki.
Har ila yau, ya ce shirin ya yi daidai da wanda aka Masar din ta taba gabatarwa a 2011.
Tags