An Ji Karar Fashewar Abubuwa A Birnin Alkahira Na Masar
(last modified Fri, 13 Jul 2018 06:31:47 GMT )
Jul 13, 2018 06:31 UTC
  • An Ji Karar Fashewar Abubuwa A Birnin Alkahira Na Masar

Labaran da suke fitowa daga birnin Alkahira na kasar Masar sun bayyana cewa an ji fashewar abubuwa a kusa da tashar sauka da tashin jiragen sama na birnin kuma an ga harshen wuta na nagawa daga yankin.

Jaridar Jumhuriyar ta kasar Masar ta nakalto jami'an gwamnatin kasar suna tabbatar da aukuwan fashewar, sannan gwamnatin kasar ta bada sanarwan dakatar da jiragen sama masu zuwa birnin ko kuma wadanda zasu tashi daga tashar tashi har zuwa wata sanarwa nan gaba.

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa fashewar ta auku ne a ajiyar makashi na tashar jiragen sama na birnin ne, amma har yanzun ba'a san dalilin aukuwar fashewar ba. 

Wannan harin ya auku ne a dai dai lokacinda majalisar dokokin kasar ta amincewa gwamnatin Abdulfata Sisi tsawaita doka ta baci dangane da harkokin tsaro a kasar ta shekara ta 2017 da ta gabata.