Pars Today
Komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi watsi da bukatar kasar Rasha na yin allahwadai da hare-haren da kasashen Amurka, Faransa da Britania suka kai kan wasu wurare a kasar Siriya a ranar Asabar.
Hukumar Kula Da Kananan Yara Ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta sanar da cewa 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram sun sace sama da kananan yara 1000 a yankunan arewa maso gabashin Nijeriya tun daga shekara ta 2013.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta soma shirin gano wadanda ke kawo tarnaki a shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, domin kakaba masu takunkumi.
Rundunar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Mali MINUSMA ta sanar da mutuwar sojojinta biyu da kuma jikkatar wasu 10 na daban a wani hari da aka kai sansaninsu na Aguelhok dake arewa maso gabashin kasar Mali.
Jami'an majalisar dinkin duniya sun sanar da cewa 'yan bindiga sun saki mutane 15 da suka yi garkuwa da su a rikicin baya-bayan nan a yankin yammacin kasar.
Firayi Ministan yahudawan mamaya na Israila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da soke yarjejeniyar bada izinin zama ga bakin haure 'yan Afrika.
Babban sakatare na MDD, Antonio Guterres ya nuna alhini kan mutuwar Winnie Madikizela-Mandela, tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela kuma shugaban gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata.
Bayan shafe shekaru 14, na aikin wanzar da zaman lafiya, tawagar MDD ta (Minul) ta fice daga kasar Laberiya a jiya Juma'a.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan bullar sabuwar masifar kwararan 'yan gudun hijira zuwa kasashen yammacin Turai.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa cikin shekaru uku na yaki a kasar Yemen an kashe fararen hula 6100, daga ciki akwai kananen yara 1500.