MDD:An Kashe Fararen Hula 6100 A Yemen
(last modified Fri, 23 Mar 2018 17:49:12 GMT )
Mar 23, 2018 17:49 UTC
  • MDD:An Kashe Fararen Hula 6100 A Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa cikin shekaru uku na yaki a kasar Yemen an kashe fararen hula 6100, daga ciki akwai kananen yara 1500.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiya ya nakalto Kate Gilmore mataimakin babban kwamishinan Hukumar kare hakin bil-adama na MDD na cewa adadin fararen hular da suka rasa rayukansu sakamakon yaki a kasar Yemen ya haura zuwa 6100 daga cikin su akwai kananen yara 1500.

Mista Gilmore ya ce mafi yawa daga cikin mutanan da aka kashe, sanadiyar ruwan bama-baman da jiragen kawancen saudiya suka kai kan al'ummar kasar ta yemen ne.

A yayin da yake ishara kan mutuwar Ryham Badaru al-zabhani mai rajin kare hakin bil-adama kuma mai sanya ido kan abinda ke faruwa a filin daga a kwamitin binciken kasar yemen, Mista Gilmore ya ce shima ya rasa ransa ne a yayin lugudar wutar da jiragen yakin kawancen saudiya suke yi a watan Favrayun da ya gabata a jahar Ta'az.

A ranar Litinin da ta gabata ce hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen ya shiga cikin shekaru.