Tawagar MDD Ta Fice Daga Laberiya
(last modified Sat, 31 Mar 2018 10:36:57 GMT )
Mar 31, 2018 10:36 UTC
  • Tawagar MDD Ta Fice Daga Laberiya

Bayan shafe shekaru 14, na aikin wanzar da zaman lafiya, tawagar MDD ta (Minul) ta fice daga kasar Laberiya a jiya Juma'a.

Tawagar ta (Minul) wacce ta kunshi dakaru 16,000 daga kasashe sama da goma, ta fice daga kasar bisa alfaharin samar da kwanciyar hankali, bayan yakin basasar tsakanin shekara 1989 da 2003 da ya daidaita kasar.

Rikicin kasar ta Laberiya dai ya hadasa mutuwar kimanin 250,000 tare da tilasta wa kashi 1/3 na mutanen kasar yin hijira.

Bayan rikicin kasar ta yi nasara shirya manyan zabuka har uku, mafi shahara kuma su ne wanda tsohuwar shugabar kasar macce ta farko a Afrika akan wannan mukami, Ellen Johnson Sirleaf ta lashe.

Sai kuma na baya bayan nan wanda ta mika ragamar mulkin kasar ga shugaba mai ci George Weah.