-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bawa Kasar Rasha Izinin Bawa Kasar Afrika Ta Tsakiya Makamai
Dec 16, 2017 06:25Kwamitin tsaro na MDD daga karshe bayan tattaunawa mai tsawo ta amincewa gwamnatin kasar Rasha ta bawa gwamnatin kasar Afrika ta Tsakiya Makamai bayan haramcin da aka dora mata tun shekara ta 2013.
-
MDD Ta Yi Watsi Da Kalaman Jakadiyar Amurka A Majalisar Kan Iran
Dec 15, 2017 15:38Mataimakin kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya bayyana cewar babu wata hujja da take tabbatar da cewa makamai masu linzamin da dakarun kasar Yemen suka harba cikin Saudiyya kirar Iran ne kuma Iran ce ta ba su.
-
Wasu Kasashen Larabawa Sun Fitar Da Daftarin Kuduri Kan Matakin Donald Trump Dangane Da Birnin Qudus
Dec 12, 2017 11:58Jakadun wasu kasashen Larabawa sun fitar da daftarin kuduri kan matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka dangane da birnin Qudus suna neman tsoma bakin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da babban zauren Majalisar.
-
Rundunar Sojin DR Congo Ta Ce Zata Maida Martani Kan Harin Da Aka Kai Kan Dakarun MDD A Kasarta
Dec 10, 2017 19:05Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da shirinta na maida martani kan harin da 'yan tawayen kungiyar "ADF" ta Uganda suka kaddamar kan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a shiyar gabashin kasarta.
-
An Kai Hare-Hare Da Makamai Masu Karfi Kan Dakarun MDD A Kongo
Dec 10, 2017 11:50MDD ta bada sanarwan cewa an kaiwa dakarunta a arewacin kasar Afrika ta Tsakiya hare-hare
-
MDD: A Kaucewa Kuskuren Lissafi Akan Korea Ta Arewa
Dec 10, 2017 07:39Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayani da a ciki ya bayyana wajabcin bude kafar tataunawa da Korea ta Arewa domin rage zaman dar-dar a yankin.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wani Kuduri Dangake Da Yankin Sahel
Dec 09, 2017 11:51Komitin tsaro na MDD ya amince da kuduri na goyon baya ga rundunar yankin Sahel ta yaki da yan ta'adda a yankin
-
M.D.D Ta Yi Gargadi Kan Cin Zarafin Bil-Adama Da Sunan Yaki Da Ta'addanci A Kasar Kamaru
Dec 08, 2017 06:19Kwamitin Yaki da Cin zarafin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan cin zarafin bil-Adama da jami'an tsaron Kamaru suke yi da sunan yaki da ta'addanci a yankunan da ake magana da harshen Turanci a kasar.
-
Kwamitin Tsaron MDD Ya Bayyana Tsananin Damuwarsa Kan Matsalar Kasar Yamen
Dec 06, 2017 18:56Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwarsa kan halin tsaka mai wuya da al'ummar kasar Yamen suke ciki, tare da jaddada bukatar dakatar da bude wuta domin aikewa da kayayyakin jin kan bil-Adama cikin kasar.
-
Yemen : Kungiyoyi Sun Bukaci A Bada Damar Shigar Da Kayan Agaji
Dec 05, 2017 16:46Wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa guda biyar, sun bukaci duk masu hannu a rikicin kasar Yemen dasu kawo karshen zubar da jini a birnin Sanaa, domin bada damar shigar da kayan agaji ga al'ummar dake cikin matsananciyyar bukata.