Yemen : Kungiyoyi Sun Bukaci A Bada Damar Shigar Da Kayan Agaji
(last modified Tue, 05 Dec 2017 16:46:28 GMT )
Dec 05, 2017 16:46 UTC
  • Yemen : Kungiyoyi Sun Bukaci A Bada Damar Shigar Da Kayan Agaji

Wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa guda biyar, sun bukaci duk masu hannu a rikicin kasar Yemen dasu kawo karshen zubar da jini a birnin Sanaa, domin bada damar shigar da kayan agaji ga al'ummar dake cikin matsananciyyar bukata.

A cikin wata sanarwa da suka fitar kungiyoyin da suka hada da Red Cross, Handicap International, Acted, Care da Medecein du Monde, sun bukaci bangarorin dake dauke da makamai da kawacen da Saudiyya ke jagoranta sun dakatar da buda wuta don kai agaji ga dubban 'yan Yemen da suka shiga tsaka mai wuya a rikicin da ya barke a baya bayan nan.

Kungiyoyin sun ce halin da ake ciki ya hana jami'ansu shiga wuraren da ake bukatar dauki don agazawa wandanda suka raunana da kuma wadanda ke da bukata dauki.

Wannan kiran dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin tsaro na MDD ke wani taron yau Talata don tattauna rikicin kasar ta Yemen.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce rikicin da ya barke tun daga ranar Juma'a data gabata tsakanin 'yan Houtsis da magoya bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh, da aka hallaka a jiya, ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 234 da kuma raunana wasu 400.