Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wani Kuduri Dangake Da Yankin Sahel
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26175-majalisar_dinkin_duniya_ta_amince_da_wani_kuduri_dangake_da_yankin_sahel
Komitin tsaro na MDD ya amince da kuduri na goyon baya ga rundunar yankin Sahel ta yaki da yan ta'adda a yankin
(last modified 2018-08-22T07:01:07+00:00 )
Dec 09, 2017 08:21 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wani Kuduri Dangake Da Yankin Sahel

Komitin tsaro na MDD ya amince da kuduri na goyon baya ga rundunar yankin Sahel ta yaki da yan ta'adda a yankin

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewa komitin tsaron ya amince da wannan kudurin ne a jiya jumma'a kuma amincewarsa  wani mataki ne na samun goyon bayan rundunar Majalisar dinkin duniya da kasar kasar Mali, da ta tallafawa runduna ta "G5" ta yankin na Sahel.

Babban sakataren MDD António Guterres bayan amincewa da kudurin, ya bukaci a gaggauta bada umurni ga rundunar majalisar dake kasar Mali , na ta bawa sabuwar rundunar ta G5 duk taimakon da ta bukata don ci gaba da yakar yan ta'adda a yankin. 

Kasashe biyar na yankin Sahel ne wato Chadi, Niger, Borkina Fasio, Mali da kuma Mauritania suka kafa rundunar G5 mai mayaka 5000 da nufin yaki da yan ta'adda a yankin