-
Rasha 2018 : Najeriya Ta Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Wasa
May 15, 2018 01:18Mai horas da 'yan wasa na tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr, ya fitar da kwarya-kwaryar sunayen 'yan wasa 30 wadanda daga cikinsu za su buga wa kasar wassani a gasar cin kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni mai zuwa a kasar Rasha.
-
Buhari Ya Yi Bayyani Kan Kudaden Sata Da Aka Kwato Na Lokacin Abacha
May 14, 2018 14:27Shugaban Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya ce gwamnatinsa zata kashe dalar Amurka miliyan 320 wadanda aka karbo daga kudaden da aka sace a lokacin gwamnatin Abacha kan shiri na musamman don tallafawa rayuwar talakawan kasar.
-
Gwamnatin Nijeriya Ta Biyan Mutane 14 Da Suka Fallasa Mata Barayin Gwamnati Hakkokinsu
May 13, 2018 01:06Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ta biya wasu mutane 14 da suka ba ta wasu muhimman bayanai da suka ba ta damar kwato biliyoyin Nairori da kuma wasu miliyoyin na daban cikin kudaden kasashen waje ladar da aka yi musu alkawarin ba su cikin shirin da gwamnatin ta fito da shi na ba da lada ga wadanda suka fallasa mata wadanda suka sace kudin kasar.
-
Buratai: Dukkan Bangarorin Biyu Suna Da Laifi A Rikicin Jihar Benue
May 12, 2018 04:45Babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya Janar Tukur Brutai ya bayyana cewa dukkan bangarorin da suke rigima da juna suna da hannu cikin laifuffukan da aka aikata a jahar Benue.
-
'Yan Sanda Sun Kashe Mutane 18 Da Kama Wasu 56 Da Suke Da Hannu Cikin Kashe-Kashen Kaduna, Zamfara
May 11, 2018 13:43Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a Nijeriya sun sanar da hallaka wasu mutane 18 masu dauke da makami da kuma kama wasu 56 da ake zargin suna da hannu cikin kashe-kashe da sace-sacen mutane a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar da kuma jihar Zamfara.
-
An Kashe Wani Jami'in Diplomasiyyar Nijeriya A Kasar Sudan
May 11, 2018 13:42Majiyoyin tsaron kasar Sudan sun bayyana cewar wasu mutane da ba a riga da an tantance su ba sun kashe wani jami'in diplomasiyyar Nijeriya a kasar ta Sudan a safiyar yau Alhamis.
-
Sufeto Janar Na 'Yan Sandan Nijeriya Ya Zargin 'Yan Majalisar Kasar Da Kokarin Bata Masa Suna
May 10, 2018 06:09Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris ya zargin 'yan majalisar kasar da kokarin bata masa suna yana mai sanar da 'yan majalisar cewar ba zai bayyana a gabansu kamar yadda suka bukata ba.
-
An Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda Biyu A Lokacin Da Suke Kokarin Kai Hari Borno
May 09, 2018 06:11Jami'an tsaro a Nijeriya sun sanar da hallakar wasu 'yan kunar bakin wake mata su biyu a yau din nan Laraba a yayin da suke kokarin kai harin kunar bakin wake wani masallaci a wajen garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
-
Sojojin Nijeriya Sun Kwato Mutane Sama Da 1000 Da Boko Haram Suka Yi Garkuwa Da Su
May 08, 2018 06:43Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta samu nasarar kwato mutane sama da 1,000 daga hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram wadanda ta yi garkuwa da su a jihar Borno.
-
Najeriya : Mutane 45 Suka Mutu A Harin Gwaska
May 07, 2018 01:20Rahotanni daga Najeriya na cewa a kalla mutane 45 suka gamu da ajalinsu a wani hari da aka kai a kauyen Gwaska dake garin Birnin-Gwari a jihar Kaduna dake kudancin kasar.