Najeriya : Mutane 45 Suka Mutu A Harin Gwaska
Rahotanni daga Najeriya na cewa a kalla mutane 45 suka gamu da ajalinsu a wani hari da aka kai a kauyen Gwaska dake garin Birnin-Gwari a jihar Kaduna dake kudancin kasar.
Majiyoyi sun ce maharan sun je kauyen ne kan babura a ranar Asabar data gabata, kuma sun fito ne daga wasu kyauyukan jihar Zamfara.
Mazauna yankin dai sun shiga cikin dimuwa, ganin irin mummunan kisan da aka yi wa mutanen ciki har da yara da mata, baya ga gidaje da dama da aka kona.
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, gwamnatin jihar Kaduna, ta ce an aike da bataliyar sojoji don kawo karshen ire-iren wannan kashe kashen.
haka kuma gwamnan Jihar ta Kaduna, Nasir el-Rufa'i, ya bayyana daukan wani mataki tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya don binciken lamarin, kuma ya bukaci hukumar agajin gaggawa ta yankin data taimaka wa wadanda lamarin ya rsutsa dasu.