-
Mutane 16 Ne Aka Tabbatar Da Mutuwarsu A Jihar Kogi A Jiya Lahadi.
Apr 23, 2018 02:22Jiradar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba a gano su waye ne ba, sun kai hare-hare a kan wasu kauyuka a jihar Kogi har kuma mutane 16 sun rasa rayukansu a jiya Lahadi.
-
Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane A Najeriya
Apr 22, 2018 14:26Wasu 'yan kunar bakin wake biyu sun kai hari masallaci a garin Bama na jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Wani Sabon Shiri Na Kawo Karshen Boko Haram
Apr 21, 2018 01:15Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kaddamar da wani sabon shiri na ganin bayan kungiyar ta'addancin nan na Boko Haram da kawo karshensa gaba daya.
-
Kalaman Shugaba Buhari Kan Matasa Ya Janyo Ce-ce Ku-ce A Najeriya
Apr 20, 2018 02:00Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na cewa matasan kasar ba suyi karatu ba, kuma ba su da aikin yi, sannan suna jira gwamnati ta samar musu ababen more rayuwa da kudin mai ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin al'ummar kasar
-
An Dawo Da Sandar Ikon Majalisar Najeriya Da Aka Sace
Apr 19, 2018 13:32'Yan sanda a Nijeriya sun dawo da sandar ikon Majalisar Tarayyar kasar da wasu 'yan daba da aka ce daya daga cikin 'yan majalisar ne ya turo su suka sace a jiya Laraba.
-
Shugaban Muhammadu Buhari Zai Halarci Taron Kungiyar ECOWAS Kan Matsalolin Kan'iyakoki A Yankin
Apr 19, 2018 01:54Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Nigeria zai halarci taron da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS a takaice zata shirya don tattauna batun kai-kawon mutane da kayayyaki tsakanin kasashen yammacin Afrika.
-
Najeriya : An Cafke Sanatan Da Ya Tura 'Yan Daba Sace Sandar Majalisa
Apr 18, 2018 12:53Rahotanni daga Najeriya na cewa, 'yan sanda kasar sun cafke sanata Ovie Omo-Agege, wanda ake zarginsa da tura 'yan daba don sace sandar majalisar dattawa.
-
'Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga-Zangar Sako Sheikh Zakzaky 115
Apr 17, 2018 00:33Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, sun sanar da cewa suna tsare da 'yan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) su 115 sakamakon dirar mikiyar da suka yi musu jiya Litinin da nufin tarwatsa jerin gwanon da suke ci gaba da yi a birnin Abujan don bukatar a sako musu shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnatin take ci gaba da tsare shi.
-
'Yansanda Sun Yi Amfani Da Karfi Wajen Tarwatsa Mabiya Mazhabar Shi'a A Abuja
Apr 16, 2018 14:27A Najeriya, Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da karfi a yau domin tarwatsa jerin gwanon da magoya bayan Harkar Musulunci da masu rajin kare hakkin bil adama suke gudanarwa a Abuja, domin yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky, yayin da wasu bayanan suka tabbatar da cewa mutane da dama sun jikkata, daya daga cikinsu yana cikin mawuyacin hali, sanan kuma an kama sama da mutane 70
-
Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Sake Bayyana Sunayen Wadanda Ake Zargi Da Satar Kudin Gwamnati
Apr 15, 2018 12:54Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake sanar da aniyarta ta sake fitar da sunayen wasu mutanen da take zargi da satar dukiyar gwamnatin kasar a shekarun baya lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.