An Dawo Da Sandar Ikon Majalisar Najeriya Da Aka Sace
'Yan sanda a Nijeriya sun dawo da sandar ikon Majalisar Tarayyar kasar da wasu 'yan daba da aka ce daya daga cikin 'yan majalisar ne ya turo su suka sace a jiya Laraba.
Tun da safiyar yau Alhamis ne dai rundunar 'yan sandan Nijeriyan ta sanar da gano sandar ikon a karkashin wata gada da ke birnin Abuja, kasa da sa'oi 24 da majalisar ta ba wa 'yan sandan na su gano inda sandar take. Rahotannin sun ce da misalin karfe 11:50 na safiyar yau din Alhamis ne mataimakin sufeto janar na 'yan sandan Nijeriyan Habila Joshak, ya mikawa akawun majalisar tarayyar Mohammed Sani-Omolori sandar ikon bayan sun gano ta.
A jiya laraba ne dai wasu 'yan daba da aka ce daya daga cikin sanatocin da aka dakatar a majalisar wato Sanata Omo-Agege ne ya turo su suka kutsa cikin majalisar da sace sandar ikon inda suka yi gaba da ita, lamarin da ya sanya 'yan sanda kama sanata din duk kuwa da ya musanta cewa shi ya turo mutanen.
A Nijeriya dai ana ci gaba da yin Allah wadai da wannan lamari da ya faru wanda yake a matsayin babban abin kunya ga majalisar da kuma kasar baki.