Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane A Najeriya
Wasu 'yan kunar bakin wake biyu sun kai hari masallaci a garin Bama na jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotani dake fitowa daga Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 6 tare da jikkatar wasu 9 na daban a wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a garnin Bama. na jiahr Borno da ke arwa maso gabashin kasar a wannan lahadi.
Mutanen da suka mutu sun hada da mahara biyu mace da namiji, da kuma masallata hudu.Hukumomin jihar sun ce an kai harin ne lokacin da ake sallar asuba.
Wannan hari na zuwa ne watani, bayan da gwamnati ta sanar da tabbatar da tsaro a garin Bama, lamarin da ya sanya mutunan garin da suka yi hijra daga garin domin cira da rayukansu koma gidajensu.
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma dai kungiyar Boko Haram tana yawan kai irin wadannan hare-hare a yankin.
Hukumomin Najeriya na ikirarin samun galaba a kan kungiyar Boko Haram, to sai dai kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan arewa masu gabas, musamman ma a jihar Borno.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Najeriya gami da raba sama da mutum miliyan biyu da mahallansu.