Pars Today
Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya, (INEC), ta bayyana cewa, babu siyasa a batun dage zagen shugabancin kasar da na ‘yan majalisu zuwa ranar 23 ga watan nan.
Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bayyana takaicinsa da yadda hukumar zabe ta dage zabubbukann da za'a gudanar a yau , musamman bayan da hukumar ta sha nanata cewa a shirye take ta gudanar da zaben
Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da dage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a yau Asabar a fadin kasar, sanarwar da ta zo 'yan sa'oi kafin fara gudanar da zaben.
Masu sanya ido daga kasashen waje a zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar Gobe Asabar a tarayyar Najeriya sun yada da shirin da hukumar zabe kasar ta yi na gudanar da zabe mai inganci a kasar.
Tsohon shugaban kasar Amurka billClinton ya santa da shugaban tarayyar Najeriya Muahmadu Buhari ta wayar tarho.
Kwanaki hudu kacal kafin a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya gobara ta lalata katunan zabe 4,695 a ofishin hukumar zabe a garin Awka na jihar Amanbara a tarayyar Najeriya a jiya Talata.
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana kaduwarta game da gobarar da ta cinye kayayyakin zabe a ofishin Hukumar Zaben Kasar, INEC da ke yankin Quan Pan a Jihar Filato, in da ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.
Spetan 'yansanda na riko a tarayyar Najeriya Mohammad Adamu ya bada umurni ga 'yansandan kasar su tabbatar da tsaro na musamman ga dukkanin ofisoshin hukumar Zaben kasar da kuma dukkan kayakin da suka shafe zabe a duk fadin kasar.
Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta sake horas da malaman zabe 846 don tabbatar da cewa sun fahinci aikinsu sun kuma gane dukkan abinda ya hau kansu su aikata a ranar zabe.
Rahotanni daga najeriya na nuni da cewa kungiyar Boko haram ta kashe sojojin kasar a wani hari data kai wani sansanin soji a arewa maso gabashin kasar.