Najeriya : Ba Siyasa A Dage Zabe Inji INEC
Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya, (INEC), ta bayyana cewa, babu siyasa a batun dage zagen shugabancin kasar da na ‘yan majalisu zuwa ranar 23 ga watan nan.
Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a binin Abuja, bayan cece-kucen da ya biyo bayan sanar da dage zaben da mako guda, Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa, dage zagen bai shafi batutuwan tsaro ba, kuma ba siyasa a cikin daukar wannan daukan matakin.
Farfesan ya ce, sun dauki matakin dage zaben ne a hukumance bayan wata ganawa da ta gudana a tsakanin jami’an hukumar ta INEC a cikin daren jiya.
Sai dai a cewarsa, matsalar isar da kayayyaki zabe da kuma gobarar da ta shafi wasu ofisoshin INEC na cikin dalilan dage zaben.
Dage babban zaben da aka shirya gudanarwa yau Asabar 16 ga watan Fabrairu 2019 ya hadassa zazzafar muhawara a kasar inda hatta manyan ‘yan takarar jam’iyyun APC da PDP, suka bayyana rashin jin dadinsu.