Pars Today
Hukuma mai kula da cututtuka masu haddasa annoba wato "the Nigeria Centre for Disease Contro" ko NCDC ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar barkewar zazzabin Lassa ya zuwa yanzu ya kai 57.
Kotun koli a jihar Rivers na tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin haramtawa jam'iyyar APC tsaida yan takara a zaben yan majalisar dokokin tarayyar da na gwamna a zabubbuka masu zuwa.
Rahotanni daga Najeriya na cewa wata mummunar gobara ta cinye wani sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin kasar.
Gabara ta cinye shaguna akalla 70 a kasuwar Yan katako a unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano a safiyar Alhamis.
Majiyar fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da cewa mutane akalla ukku ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cinkoson mutane a taron yakin neman zaben da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar Taraba.
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an samu karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin watanni 3 da suka gabata.
Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa; Wajibi ne ga kungiyoyin ba da agaji da suke karkashin Majalsiar su kara ba da taimako ga 'yan hijirar Najeriya a kasar Kamaru
Jakadan Amurka a Najeriya ya yi kira ga yan najeriya su fito don zaben shuwagabanninsu a zaben kwanaki goma masu zuwa
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu a wasu sabbin hare hare da mayakan kungiyar boko haram suka kai a kauyukan Shuwa da Kirchina, dake garin Madagali, na jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar.