MDD: Hare-Haren Boko Haram Sun Karu A Najeriya
(last modified Thu, 07 Feb 2019 07:02:22 GMT )
Feb 07, 2019 07:02 UTC
  • MDD: Hare-Haren Boko Haram Sun Karu A Najeriya

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an samu karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin watanni 3 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto hukumar dake kula da 'yan gudun hijra  ta MDD daga birnin Gavena na cewa an samu karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin watanni 3 da suka gabata, abin da ya raba mutane dubu 59 da 200 da muhallansu.

Hukumar  ta ce, karuwar hare-haren na nuna yadda kungiyar ke kara farfadowa da kuma jefa rayuwar mazauna jihohin Borno da Yobe da Adamawa cikin hadari.

Jami’in hukumar a Najeriya, Frantz Celestin ya ce, daga watan Nuwamba zuwa yanzu sun karbi mutane dubu 59 da 200 da suka tsere daga gidajensu, abin da ba su taba gani ba a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Hukumar ta ce, yanayin hazon da ake samu tsakanin watannin Nuwamba zuwa Maris, na yin illa ga ayyukan soji wajen fuskantar mayakan da ke kai hare-hare.