Pars Today
Wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, in da suka kashe mutane da dama tare da kona gidajensu a garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Gusau.
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osimbajo, na cikin koshin lafiya, bayan wani hatsari da jirgi mai saukar ungulu ya yi dashi yau Asabar a jihar Kogi.
Hukuma mai kula da yan gudun hijira ta MDD, UNHCR ta bada sanarwan cewa yan gudun hijira daga tarayyar Najeriya kimani dubu 35 suna zama a wani wuri mai aminci a cikin kasar Kamaru.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana mutane kimani 60 ne suka rasa rayukansu a wani harin da mayakan kungiyan Boko Haram suka kai a kan garin Ran na jihar Borni a ranar 28 ga watan Jenerun da ya gabata.
Gwamnonin Jihar Maradi da Zinder daga Jamhuriyar Nijar Sun isa birnin Kano na tarayyar Najeriyar don halartar yakin neman zabe wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara a birnin ranar Alhamis.
Hukumar Zabe a Najeriya ta ce tana kan matsayinta na babu dan takarar gwamna na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara.
Sakamakon wani bincike da aka gudanar a Najeriya ya yi nuni da cewa kashi 14,4 cikin dari na al'ummar kasar na tu'ammali da muggan kwayoyi.
Majalisar Dattijan Najeriya ta shigar da korafi gaban Kotun kolin kasar da ke neman fayyace mata matakan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bi wajen dakatar da alkalin alkalan kasar Walter Samuel Onnoghen.
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, babu wata kafar tafka magudi a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabairu mai zuwa.
Hukumar Zabe a tarayyar Najeriya ta bawa kungiyoyi 144 damar sanya ido a zabubbukan da za'a gudanar a cikin yan makonni masu zuwa.