Wasu Gwamnonin Nijar Sun Taya Buhari Yakin Neman Zabe A Kano
(last modified Thu, 31 Jan 2019 19:20:20 GMT )
Jan 31, 2019 19:20 UTC
  • Wasu Gwamnonin Nijar Sun Taya Buhari Yakin Neman Zabe A Kano

Gwamnonin Jihar Maradi da Zinder daga Jamhuriyar Nijar Sun isa birnin Kano na tarayyar Najeriyar don halartar yakin neman zabe wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara a birnin ranar Alhamis.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an ga gwamna Issa Musa na Zinder da kuma takwaransa na Jihar Maradi Zakari Ummaru suna sanye da manyan riguda dauke da tambarin APC wato Jam'iyyar shugaban kasa don taya shi yakin neman zabe a Kano.

Salihu Tanko Yakasai kakakin gwamnan jihar Kano Umar Ganduje ya watsa hoton gwamnonin tare da Ganduje a lokacinda suke jiran isowar shugaban kasa daga Abuja don fara yakin neman zaben. 

Yan jam'iyyun adawa dai sun fara surutu kan shigar wadannan gwamnoni cikin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan dacewarsa bisa tsarin mulkin kasar. 

Wasu masana suna ganin abinda tsarin mulki ya hana shi ne karban taimakon kudade daga kasashen waje don yakin neman zabe, amma bai yi maganar halattar yan kasashen waje a yakin neman zaman wani dan siyasa ba.