Majalisar Dattawan Najeriya Ta Garzaya Kotun Koli Kan Matakin Shugaba Buhari
(last modified Tue, 29 Jan 2019 12:32:23 GMT )
Jan 29, 2019 12:32 UTC
  • Majalisar Dattawan Najeriya Ta Garzaya Kotun Koli Kan Matakin Shugaba Buhari

Majalisar Dattijan Najeriya ta shigar da korafi gaban Kotun kolin kasar da ke neman fayyace mata matakan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bi wajen dakatar da alkalin alkalan kasar Walter Samuel Onnoghen.

A cewar majalisar ta na neman sanin ko shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki wajen sauke Onnoghen tare da maye gurbinsa da mai shari’a Tanko Mohammed.

Ka zalika Majalisar ta nemi sanin ko Shugaban na da hurumin sauke alkalin alkalai ba tare da sahalewarta ba, duba da tanadin sashe na 292 na kundin tsarin mulkin Najeriyar.

Karkashin sashen na 292 wanda ya yi bayanin kan matakan da za a bi wajen iya sauke alkalin alkalan bai fayyace matakin saukewar na din-din-din ne ko na wucin gadi ba.

Cikin wata sanarwar Majalisar mai dauke da sa hannun Yusuph Olaniyoni babban hadimin shugaban Majalisar Bukola Saraki, ta ce har yau Talata batun dakatar da alkalin alkalan Najeriyar shi ne Majalisar za ta ci gaba da tattaunawa akai.

A bangare guda kuma Yan jam'iyyar APC da ke majalisar dattawan kasar sun barratan kansu daga matakin da shugabannin majalisar suka dauka na kai shugaba Muhammadu Buhari kotu saboda dakatar da alkalin alkalan kasar.