Najeriya : Osimbajo Ya Tsira Daga Hatsarin Jirgi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35055-najeriya_osimbajo_ya_tsira_daga_hatsarin_jirgi
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osimbajo, na cikin koshin lafiya, bayan wani hatsari da jirgi mai saukar ungulu ya yi dashi yau Asabar a jihar Kogi.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 02, 2019 17:26 UTC
  • Najeriya : Osimbajo Ya Tsira Daga Hatsarin Jirgi

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osimbajo, na cikin koshin lafiya, bayan wani hatsari da jirgi mai saukar ungulu ya yi dashi yau Asabar a jihar Kogi.

Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jirgin ya yi hatsari ne a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar kasar, kuma tuni mataimakin shugaban kasar ya shiga ayyukan da suka kai shi jihar.

Jirgi mai saukar ungulu na mataimakin shugaban kasar ya yi saukar gaggawa a Kabba, amma shi da ma'aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya.

Wasu hotunan dake yawo kan shafukan sada zumunta sun nuno hoton jirgin a lokacin da ya rikito kasa, inda kura ta tirnike wurin, kafin daga bisani wasu mutane ciki har da jami'an tsaro su agaza su fiddo mutanen dake ciki.