Amurka Ta Bukaci Yan Najeriya Su Fito Don Zaben Shuwagabanninsu
(last modified Wed, 06 Feb 2019 06:40:44 GMT )
Feb 06, 2019 06:40 UTC
  • Amurka Ta Bukaci Yan Najeriya Su Fito Don Zaben Shuwagabanninsu

Jakadan Amurka a Najeriya ya yi kira ga yan najeriya su fito don zaben shuwagabanninsu a zaben kwanaki goma masu zuwa

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto Mr Stuart Symington yana fadar haka a jiya Talata ya kuma kara da cewa yakamata yan najeriya su san hakkinsu su fito don zaben shuwagabanninsu. 

Symington ya bayyana haka ne a shafinsa na Tweter a jiya Talata ya kuma kara da cewa yakamata yan Najeriya su yi aiki tare da tabbatar da tsarin democradiyya ta tabbata a kasar. 

Jakadan ya ce gwamnatin Amurka tana fatan zabe mai zuwa a tarayyar Najeriya zai kasance mai inganci da yenci da kuma rashin magudi. 

Dole ne atabbatar da cewa babu wani dan siyasa, ko jami'in tsaro ko wani daban wanda zai ja ra'ayin wani don zabar wani takara a zaben.

Yace zabe daya ne daga cikin bangarorin Democradiyya , amma yadda ake tafiyar da kasa da yadda shuwagabannin suke hulda da yan kasa duk suna cikin tsarin Democradiyya.

A ranar 16 ga watan feberern da muke ciki ne za'a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun tarayyar a tarayar Nigeriya.