-
Don Tabbatar Da Tsaron Makarantu, Shugaban Dakarun Civil Defence Ya Koma Jihar Borno
Mar 04, 2018 02:23Babban kwamandan dakarun tsaro na Civil Defence na Nijeriya, Abdullai Gana, ya koma jihar Borno da zama, biyo bayan umurnin da shugaba Muhammadu Buhari Nijeriya ya bayar na ya koma can din don taimakawa sauran hukumomin tsaron kasar tabbatar da tsaro a yankin da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addancin Boko Haram.
-
MDD Ta Dakatar Da Aikin Agaji A Arewa Maso Gabashin Nijeriya Bayan Harin B/Haram
Mar 04, 2018 02:22Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da dakatar da ayyukan agajin da take gudanarwa a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya bayan wani hari da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai da yayi sanadiyyar mutuwar wasu jami'an ba da agajinta su 3 da kuma batar wasu ukun na daban da ake zaton an sace su ne.
-
MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Ma'aikatan Bada Agaji Da Kungiyar Boko Haram Ta Yi Nigeriya
Mar 03, 2018 09:01Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi tofin Allah tsine kan harin da kungiyar Boko Haram ta kai garin Rann na jihar Borno a tarayyar Nigeriya tare da kashe ma'aikatan bada agaji.
-
Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Mutane Akalla 4 A Garin Rann Na Jihar Bornon Nigeriya
Mar 02, 2018 08:34'Yan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani mummunan harin wuce gona da iri kan garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya, inda suka kashe mutane akalla hudu.
-
Najeriya : Cutar Zazzabin Lassa Ta Yi Ajalin Mutum 72
Mar 01, 2018 07:47Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa mutane 72 ne suka rasa rayukansu a Najeriya, sanadin kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
-
Najeriya : An Kafa Kwamitin Binciken Sace 'Yan Makarantar Dapchi
Feb 28, 2018 07:42Gwamnatin Najeriya, ta sanar da kafa wani kwamitin da zai binciki hakikanin abunda ya faru kan sace 'yan matan makarantar sakadaren Dapchi dake jihar Jobe a arewa maso gabashin kasar.
-
Jami'an Sojin Najeriya Da Na Kamaru Sun Ce Sun Kashe 'Yan Boko Haram 35
Feb 27, 2018 15:59Rundunar sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram ta ce a wani farmaki na hadin gwiwa da suka kai tare da sojojin Kamaru a kan wuraren buyar 'yan Boko Haram, sun kashe 35 daga cikin mayakan kungiyar.
-
Nakiya Ta Kashe Sojan Najeriya Guda A Jihar Borno
Feb 27, 2018 04:38Majiyar sojojin Najerya a jihar Borno ta bayyana cewa soja guda ya rasa ransa a lokacinda motar da yake tukawa ta taka nakiya a gefen tati a wani wuri a jihar.
-
Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Sanar Da Tura Karin Jiragen Sama Don Neman 'Yan Matan Dapchi
Feb 26, 2018 02:16Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta kara tura jiragen sama da sauran na'urorin bincike zuwa yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriyan don ci gaba da neman 'yan matan makarantar mata ta Dapchi da suka bace bayan wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar a makon da ya wuce.
-
Iyayenda Yayansu Suka Bace A Jihar Yobe Zasu Shiga Kungiyar "A Dawo Da Yan Matammu" Ta Kasa.
Feb 24, 2018 08:23Iyayen yan makaranta yan mata wadanda aka sace a makarantar Dapchi ta jihar Yobe sun bayyana anniyarsu ta shiga kamfain na "A dawo da yan matammu" wanda ya sami karbuwa a fagen kasa da kasa don dawo da yan mayan makarantar Chibok da aka sace a baya.