Najeriya : Cutar Zazzabin Lassa Ta Yi Ajalin Mutum 72
Mar 01, 2018 07:47 UTC
Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa mutane 72 ne suka rasa rayukansu a Najeriya, sanadin kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
Mutane 317 da aka yi amannar cewa sun kamu da cutar, a cewar rahoton na hukumar WHO.
Kwayoyin cutar mai saurin kisa sun yadu ne a jahohin kasar 18, tun bayan da aka samu rahoton bullar cutar a farkon wannan shekara ta 2018, wanda kuma ya linka adadin wadanda aka samu a bara.
A halin yanzu dai ana sanya ido kan wasu mutane kimanin 2,845 da ake kyautata zaton sun yi mu'amula da wadanda suka kamu da cutar, kamar yadda hukumar ta WHO ta rawaito daga hukumar magance bazuwar cutuka ta Najeriyar (NCDC).
Tags