Nakiya Ta Kashe Sojan Najeriya Guda A Jihar Borno
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28605-nakiya_ta_kashe_sojan_najeriya_guda_a_jihar_borno
Majiyar sojojin Najerya a jihar Borno ta bayyana cewa soja guda ya rasa ransa a lokacinda motar da yake tukawa ta taka nakiya a gefen tati a wani wuri a jihar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 27, 2018 04:38 UTC
  • Nakiya Ta Kashe Sojan Najeriya Guda A  Jihar Borno

Majiyar sojojin Najerya a jihar Borno ta bayyana cewa soja guda ya rasa ransa a lokacinda motar da yake tukawa ta taka nakiya a gefen tati a wani wuri a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Sahara reporters a shafinsa na yanar gizo ya nakalto majiyar tana cewa sojan da ya rasa ransa yana kan aikinsa na sintiri ne a jiya litinin a lokacinda motarsa ta taka nakiyan da aka bisne a gefentoti, ya kuma yi sanadiyar kasheshi nan take..

Mayakan kungiyar boko haram ce ake tuhuma da bisne nakiyar duk da cewa babu wata kungiya da ta bayyana alhakin bisne makamin wanda ya yi sanadiyyar kissan.

Mayakan na boko haram dai sun koma dai sun koma yakin sari ka noke ko kuma kunan makin wake da kuma bisne nakiyoyi irin wannan bayan da sojojin shirin "Operattion lafiya Dole " na sojojin kasar ya takura masu. Har ya kai ga da daa daga cikinsu suna mika mai ga sojojin.