-
Najeriya : An Kaddamar Da Gagarimin Kamfe Na Rigakafin Cutar Shawara
Jan 26, 2018 01:10Hukumomin A Najeriya sun kaddamar da wani gagarimin kamfe na rigakafin cutar shawara wanda ba'a taba yin irinsa ba a wannan kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.
-
Osinbajo: Abin Da Ya Damu Buhari Shi Ne Cika Alkawarin Da Yayi Wa 'Yan Nijeriya Ba Zaben 2019 Ba
Jan 25, 2018 14:14Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar babban abin da shugaban Nijeriyan, Muhammadu Buhari, ya sa a gaba a halin yanzu shi ne kokari wajen ganin ya cika alkawarin da yayi wa 'yan kasar a lokacin yakin neman zaben 2015 ba wai batun zaben shekara ta 2019 ba.
-
Sama Da 'Yan Gudun Hijiran Kamaru 43,000 Suka Shigo Nijeriya Sun Tsira Da Rayuwarsu
Jan 25, 2018 14:13Jami'ai a Nijeriya sun bayyana cewar sama da 'yan gudun hijira 'yan kasar Kamaru 43,000 ne suka gudu daga kasar zuwa Nijeriya don tseratar da rayukansu daga dirar mikiyan da gwamnatin kasar ta ke yi wa 'yan yankin maso magana da turancin Ingilishi 'yan aware.
-
Najeriya : Gwamnatin Buhari Ta Mayarwa Obasanjo Martani
Jan 25, 2018 06:47Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani dangane da kiran da tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari na cewa kamata ya yi ya je ya huta kada ya tsaya takara a zaben 2019.
-
Buhari Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Hare-Haren Mahara A Kasar Nan Ba Da Jimawa Ba
Jan 23, 2018 01:43Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba hare-haren da wasu 'yan bindiga da ake cewa makiyaya ne suke kai wa wasu sassa na kasar zai kawo karshe sakamakon irin matakan da gwamnatinsa take dauka.
-
Jami'an Custom A Nigeria Sun Kama Jarkokin Mai 22,000 Da Aka Yi Fasa Korinsu Zuwa Cikin Kasar
Jan 22, 2018 15:34A dai dai lokacinda kamfanin sarrafa man fetur a tarayyar Nigeria NNPC yake kokarin samar da isasshen man fetur a cikin kasar hukumar hana fasa kori ta kasar wato Custon ta bada sanarwan kama jarika 22,000 na man fetur wadanda aka shigo da shi kasar ba bisa ka'ida ba.
-
An Kai Hari Kan Ma'aikatan Hako Mai A Kudancin Najeriya
Jan 20, 2018 08:19Kakakin 'yan sandar jahar Delta da ke kudancin Najeriya ya sanar da kai harin kan wasu ma'aikatan hako danyen man fetur a yankin.
-
Yansanda Sun Kama Mutane 3 Masu Harhada Bama-Bamai A Jihar Edo
Jan 20, 2018 02:45Kwamishinan yansanda a jihar Edo ya bada sanarwa kama mutane uku tare da kayaki da sinadaran harhada bama-bamai dukkaninsu yan jihar Kogi.
-
An Tura 'Yan Sanda Na Musaman Domin Ceto Turawan Da Aka Sace A Jahar Kaduna
Jan 19, 2018 08:14Rundunar yansanda a jihar Kaduna da ke tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman domin ceto wasu ƙwararrun turawa 4 kan samar da makamashi ta hanyar hasken rana da aka yi garkuwa da su a jihar, wadda ke yankin arewacin ƙasar.
-
Kotu A Nijeriya Ta Tabbatar Da Kungiyar IPOB A Matsayin Kungiyar Ta'addanci
Jan 19, 2018 02:22Babbar kotun Tarayya a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya ta yi watsi da karar da kungiyar nan ta tsageran Inyamurai masu son kafa kasar Biafra ta IPOB ta shigar inda ta tabbatar da ita a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.