Yansanda Sun Kama Mutane 3 Masu Harhada Bama-Bamai A Jihar Edo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27431-yansanda_sun_kama_mutane_3_masu_harhada_bama_bamai_a_jihar_edo
Kwamishinan yansanda a jihar Edo ya bada sanarwa kama mutane uku tare da kayaki da sinadaran harhada bama-bamai dukkaninsu yan jihar Kogi.
(last modified 2018-08-22T07:01:18+00:00 )
Jan 20, 2018 02:45 UTC
  • Yansanda Sun Kama Mutane 3 Masu Harhada Bama-Bamai A Jihar Edo

Kwamishinan yansanda a jihar Edo ya bada sanarwa kama mutane uku tare da kayaki da sinadaran harhada bama-bamai dukkaninsu yan jihar Kogi.

Jaridar Sahara Reporters ta Nigeria a shafinta na yanar gizo ta nakalto kwamishinan yansandan Babatunde Kokumo   ya bayyana cewa mutanen ukku su ne Idris Ibrahim,da shekara 22 a duniya, Zainab Ibrahim da kuma Oyeza Ibdul. Ya kuma kara da cewa wanda ake ganin shi ne shugabansu Hassan Abdulmalik mijin Oyeze ya tsere bayan da masu tsaron yankin nasu suka hanashi gudu da motarsa.

Kwamishinan ya kara da cewa an gano abubuwa harhada boma-bomai da kuma wasu makamai daban daban wadanda suka hada da bindigogi da kuma wasu kananan makamai.

kwamishinan ya ce suna kara bincike don sanin wadanda suke wa aiki, da kuma inda suke kai makaman da suka harhadawa.