Najeriya : An Kaddamar Da Gagarimin Kamfe Na Rigakafin Cutar Shawara
Hukumomin A Najeriya sun kaddamar da wani gagarimin kamfe na rigakafin cutar shawara wanda ba'a taba yin irinsa ba a wannan kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.
Kimanin mutane miliyan 25 ne za'ayi wa riga kafin cutar kafin nan da karshen wannan shekara.
Tun daga watan Satumba da ya gabata mutane 45 ne cutar ta yi ajalisu a Najeriya.
Babban burin da shirin wanda na hadin gwiwa ne da hukumar lafiya ta Duniya da asusun kula da yara na MDD (Unicef) shi ne kawar da cutar ta shawara a Najeriya kafin shekara 2026 a cewar hukumomin lafiya na kasar.
Tuni dai aka kaddamar da kamfe na rigakafin cutar a jihohi uku na kasar da suka hada da Zamfara, Kogi da kuma Kwara.
Nan gaba kuma za a fadada shirin zuwa jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar musamen a sansanonin 'yan gudun hijira Boko haram.