-
Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-Kashen Binuwai
Jan 13, 2018 13:37Sufeto Janar na 'yan Sandan Nijeriya Ibrahim Idris ya bayyana cewar rundunar tasa ta shirya wajen kawo karshen kashe kashen da ke faruwa a jihar Binuwai na kasar yana mai cewa zai kai ziyara wasu garuruwa da rikicin yayi tsanani don gane wa idanuwansa abin da ke faruwa bayan da gwamnan jihar yayi zargin a nan ne aka tara masu kai hare-haren.
-
Sheikh El-Zakzaky Ya Gana Da Manema Labarai A Karon Farko
Jan 13, 2018 12:27Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar shugaban kungiyar Harkar Musulunci a kasar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya gana da manema labarai karon farko tun bayan da aka kama shi shekaru biyu da suka gabata inda ya bayyana cewar yana nan a raye kuma lafiyar lau inji kafafen watsa labaran.
-
Dubban Dubatan Malaman Makaranta A Kaduna Sun Gudanar Sa Zanga-Zangar Lumana
Jan 12, 2018 03:01Akalla sama da mutane 36,000 ne na gamayyar kungiyoyin malamai da na yan kwadago suka gudanar da zanga-zangar a kaduna duk tare da gargadin gwamnatin na kada su yi hakan.
-
Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsaro Ta NIA
Jan 11, 2018 02:18Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya nada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasar (NIA) wanda zai maye gurbin tsohon shugaban da aka kora.
-
Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Wasu Mata 'Yan Kunar Bakin Wake Da Kuma Kama Guda
Jan 10, 2018 07:53Sojojin Nijeriya a garin Gamboru-Ngala na jihar Borno sun bayyana cewar sun sami nasarar dakile wani gagarumin shiri na kai hari garin a yayin da suka sami nasarar hallaka wasu mata 'yan kunar bakin wake su biyu da suka yi kokarin shigowa garin dauke da ababe masu fashewa da suka yi jigida da su.
-
Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh El-Zakzaky A Najeriya
Jan 08, 2018 15:43Al'ummar musulmi mabiya mazhabar Shi'a almajiran sheikh Ibrahim Elzakzaky na ci gaba da gudanar da zanga -zanga neman a saki jagoran na su domin yi masa magani
-
Mutum Guda Ya Rasu Yayin Zanga-Zangar Kiran A Saki Sheikh Zakzaky A Kaduna
Jan 08, 2018 07:51Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar mutum guda ya rasu wasu kuma sun sami raunuka a lokacin da 'yan sanda suka fada wa 'yan kungiyar Harkar Musulunci ta kasar da suka fito don gudanar da zanga-zangar a saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnatin Nijeriya ta ke ci gaba da tsare shi sama da shekaru biyun da suka gabata.
-
A Yau Litinin Ne Malaman Makaranta A Kaduna Za Su Fara Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani
Jan 08, 2018 03:35A yau litinin ne kungiyar malaman makarantu ta Najeriya reshen jihar kaduna zata fara yajin aikin na sai baba ta gani don nuna rashin amincewarsu da kokarar malamai kimani 22,000 wanda gwamnan jihar Ahamad El-Rufa'i yayi.
-
Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Ce Kada A Maida Rikicin Kabilanci A Kasar Zuwa Na Siyasa
Jan 08, 2018 03:10Gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi kira ga yan siyasa kada su maida rikice-rikicen kabilanci da ke faruwa a wasu sassa na kasar hanyar cimma burinsu na siyasa.
-
Najeriya Za Ta Kara Kaimin Jigilar 'Yan Kasar Mazauna Kasar Libya
Jan 07, 2018 03:00Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar a jiya asabar cewa za ta kara kaimin dawo da 'yan kasar daga Libya