Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsaro Ta NIA
(last modified Thu, 11 Jan 2018 05:48:58 GMT )
Jan 11, 2018 05:48 UTC
  • Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsaro Ta NIA

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya nada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasar (NIA) wanda zai maye gurbin tsohon shugaban da aka kora.

A wata sanarwa da fadar shugaban Nijeriyan dauke da sanya hannun mai ba wa shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adeshina, ta ce shugaba Buhari ya nada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar ta NIA wacce take kula da lamurran da suka shafi leken asiri na kasashen waje.

Mr. Ahmed Rufai Abubakar dai ya kasance tsohon ma'aikacin Ma'aikatar harkokin waje ne na Nijeriyan sannan kuma kafin a ba shi wannan mukamin ya kasance mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin kasashen waje.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2017 ne dai shugaba Buharin ya kori tsohon shugaban hukumar ta NIA Ambassador Ayo Oke bisa zargin rashawa da ta'annuti ga tattalin arzikin kasar bayan da aka gano wasu makudan kudade sama da dala miliyan 43 da aka boye a wani gida a Lagos mallakin tsohon daraktan duk kuwa da ya  yi ikirarin mallakar hukumar ce.