Dubban Dubatan Malaman Makaranta A Kaduna Sun Gudanar Sa Zanga-Zangar Lumana
Akalla sama da mutane 36,000 ne na gamayyar kungiyoyin malamai da na yan kwadago suka gudanar da zanga-zangar a kaduna duk tare da gargadin gwamnatin na kada su yi hakan.
Jaridar Leadaship ta hausa a Najiraya ta bayyana cewa Akalla sama da mutum dubu 36, 000, ne na gamayyar kungiyoyin Malamai da na ‘yan kwadago suka gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar Kaduna, duk da gargadi da barazanar da Gwamnatin Jihar ta yi a kan hana gudanar da zanga-zangar. Tun da misalin karfe 6 na safiyar jiya Alhamis ne dakarun hadin gwiwar jami’an tsaro suka zagaye Sakatariyar ofishin kungiyar kwadago ta kasa, reshen Jihar Kaduna da ke titin Indifenda, domin ganin sun tarwatsa ‘ya’yan kungiyar da ke shirin gudanar da zanga-zangar.
Jiradar ta kara da cewa masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye dauke da rubutu kmar haka"“babu wani mahaluki da zai kori ma’aikata sama da dubu 57 face wani mutum marar imani a cikin zuciyarsa”.
Daga karce an kammala zanga znagar a gidan gwamnatin inda shuwagabannin malaman makarantar da kuma na kungiyar kwadago suka yi jawabai aka watse.