Pars Today
Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar cewa jiragen sojinta sun kai jerin hare hare kan wasu sansanonin 'yan ta'adda a Aleppo, bayan da 'yan ta'addan suka kai hari da makamai masu guba a yankin.
Sojojin kasar Rasha sun sanar da mayar 'yan kasar Siriya dake gudun hijra a kasashen waje kimanin dubu 270 gida.
Rundunar tsaron kasar Rasha ta dauki matakin rufe wasu manyan tashoshin jiragen kasa guda biyu da suke birnin Moscow fadar mulkin kasar saboda da matakan tsaro da nufin kare lafiyar jama'a.
Yau Juma'a, kasar Rasha na karbar batuncin wani taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya a kasar Afganistan.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa: Kungiyoyin 'yan ta'adda da suke lardin Idlib na kasar Siriya suna ci gaba da karya yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a lardin.
Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kwamitin tsaro na MDD ya gudanar da taron sirri kan kasar Korea ta Arewa a wannan alhamis.
Ministocin harkokin wajen kasashen Spain da Rasha sun soki siyasar Amurka musamman kan takunkuman data sake kakaba wa Iran, tare da yin allawadai da sharudan da Amurka ta gindaya kan kasashen dake ci gaba da yin hulda da Iran din.
Shugaba Bashar al-Assad na Siriya, ya tattauna batun kafa kwamitin tsara kundin mulkin kasarsa, da jakadan musamman na shugaban Rasha Alexander Lavrentiev, wanda ke ziyarar aiki a kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa tana goyon bayan shirin zaman tattaunawan sulhu kan kasar Yamen karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.
Shugabannin kasashen Rasha, Faransa, Turkiyya da kuma Jamus na wani taro a birnin Santanbul kan batun Siriya.